An hallaka 'yan kungiyar da dama a lokacin samamen inda aka gano makamai da kayayyakin na'urori da aka lalata su a lokacin samamen da sojin suka aiwatar a garin Gudumbali a gundumar Kukawa, kamr yadda kakakin rundunar Kanar Sani Usman ya tabbatar ma Xinhua.
Ya ce sojojin Najeriya har yanzu suna fatattakar 'yan kungiyar a maboyar su dake dajin Sambisa, daya daga cikin sansanoni mafi girma na horon kungiyar, a cewar kakakin sojin. Lakabin wannan samame shi ne "Lafiya Dole" domin kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Shugaban kasar Muhammadu Buhari a makon jiya ya bada umurni ga sabbin hafsoshin tsaron kasar da su tabbatar da kawo karshen ayyukan kungiyar ta boko haram a cikin watanni 3. (Fatimah Jibril)