in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage damar sakin Oscar Pistorius
2015-08-20 09:55:45 cri

Ministan shari'ar kasar Afirka ta Kudu Michael Masutha, ya ba da umarnin dage batun sakin shahararren 'dan wasan tseren nakasassun nan Oscar Pistorius daga gidan kaso, bayan da tsagin shari'ar kasar mai lura da yafiya ya bayyana dacewar hakan.

Mr. Masutha ya bayyana dakatar da sakin Pistorius ne bayan da wata kungiyar kare hakkin mata ta gabatar da koken rashin amincewa da sakin 'dan wasan. Yana mai cewa, ba a bi ka'ida ba wajen yanke wannan shawara.

Idan dai ba a manta ba a ranar 21 ga watan Octobar bara ne aka yankewa Pistorius hukuncin daurin shekaru 5, bayan da aka same shi da laifin kisan budurwasa mai suna Reeva Steenkamp bisa kuskure. Sai dai a 'yan kwanakin da suka gabata, sashen shari'ar kasar mai lura da yafiya da gyaran halayya, ya amince da a saki Pistorius, duba da yadda halayyarsa ta sauya bayan ya shafe 'yan watanni a kurkuku.

Kafin dakatar da wannan mataki, sashen ya ayyana cewa, za a saki Oscar Pistorius ne a ranar Juma'ar nan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China