A jiya ne babbar kotun arewacin Gauteng da ke birnin Pretoria a kasar Afirka ta Kudu ta samu wasu 'yan sanda 8 da laifin kashe wani 'dan kasar Mozambique mai suna Mido Macia a shekarar 2013.
A lokacin da yake yanke hukunci, alkalin kotun Bert Bam ya bayyana cewa, duniya ta ga yadda wadanda ake zargin suka rika jan Mido Marcia a kasa, kana suka lakada masa duka har sai da ya mutu.
Bugu da kari, alkalin kotun ya karyata ikirarin da 'yan sandan suka yi cewa, Macia ya far musu ne a kokarin yi musu fashi da makami, inda suka yi kokarin kama shi a yankin Daveyton a Johannesburg a shekarar 2013.
Alkali Bam ya ce, dukkan 'yan sandan 8 suna da hannu a jan Macia a bayan motar 'yan sanda, da kuma yadda aka gallaza masa ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2013 a ofishin 'yan sanda da ke Daveyton.
Mutuwar Macia dai ta janyo hankulan jama'a a ciki da wajen kasar, bayan da aka nuna hoton bidiyon yadda 'yan sanda suka rika jan Macia a kan titunan birnin Daveyton a shafin sada zumunta na YouTube.(Ibrahim)