in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta tura tawagar dalibai mafi yawa zuwa Sin
2015-08-25 10:26:11 cri

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta tura tawagar dalibai 53 zuwa kasar Sin, kuma wannan shi ne adadi mafi girma da kasar Afrika ta Kudun ta taba turawa don yin karatu a kasar Sin.

Mataimakin ministan ma'aikatar ilmi mai zurfi na Afrika ta Kudu Mduduzi Manana shi ne ya tabbatar da hakan, ya ce, gwamnatin kasar Sin ne ta samar da guraben karo ilmi ga daliban inda za su yi karatu a fannoni daban daban.

A jawabinsa yayin bikin ban kwana da daliban, Mista Manana ya ce, kasahen biyu sun dade suna cin gajiyar dangantakar dake tsakanin su, kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu na taimakawa nahiyar Afrika, da ma duniya baki daya.

Mataimakin daraktan sashen yada labarai da sadarwa na Afirka ta Kudu Busiswa Nongogo, ya ce, daliban za su karanci fannoni daban daban da suka hada da fannin aikin likita, da kimiyya, da aikin gona da tattalin arziki da yaran Sinanci da dai sauransu.

Haka zalika ya gargadi daliban da su yi amfani da ilminsu don taimakawa wajen gina kasarsu.

Ya zuwa yanzu sama da dalibai dubu 1 ne 'yan asalin Afrika ta Kudu ke karatu a kasar Sin a cikin 'yan shekarun da suka gabata. (Ahmad Fagam).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China