in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na son kara koyi da tsarin Sin na kafofin watsa labarai
2015-07-23 11:21:01 cri

Kasar Afrika ta Kudu na son kara koyi da kasar Sin da kuma ci gabanta game da harkokin watsa labarai, in ji ministar sadarwar Afrika ta Kudu, Faith Muthambi.

Madam Muthambi ta yi bayani a kan wannan batu kafin wata ziyarar aiki a kasar Sin da aka tsai da daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Yuli, da zummar bunkasa dangantaka tare da takwarorinta na kasar Sin kan batutuwa da dama dake da nasaba da sadarwa.

Haka kuma ministar ta ce, za ta yi amfani da wannan ziyara domin fahimtar yadda matsayin musanyar labarai da sanin aiki ke taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki, tare da kokarin gaggauta ci gaban sauyi kan zamantakewar al'umma, da ma tattalin arziki.

A tsawon wannan ziyara ta kwanaki biyar a Beijing, madam Muthambi za ta gana da manyan jami'an babbar hukumar aikin jarida, wallafa jaridu, rediyo, fina finai da talabijin ta kasar Sin da kuma shugabannin cibiyar watsa labarai.

Wannan ziyara dai za ta kasance wata babbar dama domin kara koyo kan kasar Sin da ci gaban masana'antar harkokin talabijin. Haka kuma wata dama na aza harsashe kan musanya da dangantaka a wasu fannoni tsakanin kasashen biyu, in ji madam Muthambi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China