in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta nanata kudurin na samun makamashin nukiliya
2015-07-15 09:48:15 cri

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta sake nanata kudurinta na ganin ta samu makamashin nukuliya a wani bangare na magance matsalar makamashi da kasar ke fuskanta.

Mataimakin darekta mai kula da harkokin makamashin nulikiya a sashen samar da makamashi na kasar (DOE) Zizamele Mbambo ne ya bayyana hakan a jiya Talata a birnin Durban lokacin da yake zantawa da manema labarai game da shirin kasarsa na karfafa hadin gwiwa da kasashe masu karfin nukiliya.

Zizamele ya ce, gwamnati na nan a kan bakarta na ganin ta magance matsalar makamashi da kasar ke fuskanta ta hanyar sabon shirin nan na samar da makamashi ta hanyar amfani da karfin nukiliya.

Bugu da kari, gwamnatin ta himma wajen tabbatar da ganin ta samar da hasken wutar lantarki mai dorewa a wani bangare na kaucewa fitar da iska mai gurba muhalli.

Ya ce, sabon tsarin samar da makamashi na kasar ta hanyar amfani da karfin nukiliya zai kuma samar da guraben aikin yi ga kasar, kara kwarewa, bullo da masana'antu, tare da kara samun dabaru a harkokin tattalin arziki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China