Bude wannan hanya muhimmin mataki ne da kamfanin na Southern Airlines na kasar Sin ya dauka, domin kara hadin gwiwar harkar zirga-zirgar jiragen sama a yankin, da bin manufofin "Ziri daya da hanya daya" na kasar Sin, da kuma biyan bukatu na mu'amala a tsakanin jama'ar Sin da Kenya.
A shekarun baya baya nan, ana samun bunkasuwa cikin sauri a fannin mu'amalar tattalin arziki da cinikayya da al'adu a tsakanin Sin da Afirka. Kuma yawan fasinjojin dake hawa jiragen sama a tsakanin Sin da Afirka na karuwa da kashi 15 cikin dari a kowace shekara, adadin da ya kai miliyan 1 da dubu 500 kan shekara guda.
Kaza lika Sin ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin jigilar da kaya a tsakaninta da kasashen Afirka 17, kamarsu Habasha, da Afirka ta Kudu, kuma ta sa hannu kan daftarin yarjejeniya a wannan fanni tare da kasashen Afirka 6 ciki hadda Seychelles.
Jiragen sama masu lamba CZ633/634 na kamfanin Southern Airlines na kasar Sin, za su rika tashi sau uku a ko wane mako zuwa birnin Nairobi daga birnin Guangzhou, tafiyar da tsayin ta ya kai sa'oi 11. (Zainab)