A ranar Laraba ne ministar shari'a ta kasar Amurka Loretta Lynch ta gudanar da taron manema labaru, inda ta yi bayani kan wannan batun na kama manyan jami'an hukumar FIFA da kamfanoni 14 dake shafar hukumar, inda ta ce, kasar Afirka ta Kudu ta ba da cin hanci da ya kai dala miliyan 10 ga wani mataimakin shugaban hukumar FIFA don samun iznin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2006 da na 2010.
A da Ministan harkokin wasanni na kasar Afirka ta Kudu Fikile Mbalula ya musunta wannan batu a wani taron manema labarai na musamman da ya kira a ranar 28 ga wata inda ya ce, ma'aikatar harkokin wasanni da gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ba su ba da wannan kudi ba.
Kana minister a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu Jeff Radebe ya bayyana a wannan rana cewa, kasarsa ba ta aikata wannan laifi yayin da take neman samun iznin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010 ba. Kuma mashahurin kamfanin akanta na Ernst & Young ya binciki dukkan takardaun mu'amular kudaden kasar bayan kammala gasar cin kofin duniya na shekarar 2010 da kasar ta karbi bakunci.(Zainab)