in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalar rashin aikin yi na cigaba da tabarbarewa a Afrika ta Kudu
2015-07-30 10:37:14 cri

Adadin mutanen dake zaman kashe wando ya karu da dubu 321, inda ya wuce daga miliyan 4.9 zuwa miliyan 5.2 a farkon watanni shida na shekarar 2015, a cewar wani binciken watanni uku da cibiyar da kula da aikin yi ta kasar ta fitar a ranar Laraba.

Wadannan alkaluma ba su hada ba da mutane miliyan 2.4 dake neman aiki yi da suka yi ragon kaya wajen neman aiki amma suka yi watsi da neman a farkon watanni shida na shekarar.

Wannan bincike, da hukumar kididdaga ta Afrika ta Kudu (Stats SA) ta gudanar, na nazari kan kasuwar neman aiki yi na mutane masu shekarun haihuwa 15 zuwa 64 dake rayuwa a Afrika ta Kudu.

Sakamakon binciken na watanni shida na biyu na nuna cewa, bisa miliyan 36 na mutanen dake karfin yin aiki, miliyan 15.7 suna da aiki yi, miliyan 5.2 suna zaman kashe wando, kana miliyan 15.1 ba su da karfin tattalin arzikin tafiyar da harkokinsu.

Wannan bangare na wakiltar adadi mafi rinjaye na aiki yi, kimamin kashi 69.2 cikin 100, a yayin da fannin noma yake kasa sosai da kashi 5.6 cikin 100.

Kimanin kashi 16 cikin 100 na mutane ba su da aiki ta fuskar tattalin arzki suna cikin rukunin mutanen da suka nuna kasau wajen neman aiki, a yayin da kuma kashi 80 cikin 100 daga cikinsu suna aiki bisa wasu dalilai, misalin a matsayin dalibai ko mace ko namiji mai zaman gida.

Da suke mai da martani kan wadannan alkaluma na baya baya, jam'iyyar Ammoa (DA) ta yi kira da a shirya wata muhawarar kasa domin tattauna matsalar rashin aikin yi.

Dole a amince cewa, akwai babbar matsala ta rashin aiki yi a Afrika ta Kudu, in ji David Maynier, ministan kudin Afrika ta Kudu, na jam'iyyar adawa ta DA.

Ganin cewa mutane miliyan 5.2 ba su samun aikin yi, na tada hankali matuka, musammun ma idan aka dauki cewa, ga kowa ne mutum da ya rasa aikin yi, mutane hudu ne ke dogaro da shi, in ji mista Maynier. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China