Rikici na sabon zagaye ya faru a garin Isipingo dake kusa da birnin Durban a ranar 25 ga watan Maris, daga baya ricikin ya bazu zuwa sauran garuruwa. Ya zuwa yanzu, an lalata da kwace kantunan fiye da dari daya da mutanen kasashen waje suka mallaka tare da kwatan kayayyakin dake ciki, lamarin da ya sanya 'yan mutanen kasashen waje fiye da dubu daya sun suka rasa gidajensu, kuma mutane fiye da goma a cikinsu sun ji rauni a samakaon rikicin, sannan an tabbatar da mutuwar daya daga cikinsu domin rauninsa ya yi tsanani.
Shugaba Zuma ya yi kashedi ga jama'ar kasar Afirka ta Kudu cewa, ba dukkan mutanen kasashen waje sun kaura zuwa kasar ba bisa doka bake zama a kasar ba tare da izini ba, mutane da dama a cikinsu suna da takardun visa da aka samu bisa doka, wadanda suka bada gudummawa wajen sa kaimi ga raya tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu, kana suna bin dokokin kasar, don haka, a cewar shugaba Zuma jama'ar kasar ba su da kowane wani dalili nada kai hari ga mutane daga kasashen waje.
Shugaba Zuma ya ce, gwamnatin kasar za ta yanke hukunci gayaki da mutanen da suka kaura zuwa kasar ba bisa doka ba, musamman ma wadanda suka aikata laifin yin ciniki ba bisa doka ba da kuma sauran laifuffuka, kana za ta yaki daa yanke hukunci ga al'ummar kasar da suka halarci aikin kai hari ga mutanen kasashen waje da lalata kantunansu.
Hakazalika kuma, Zuma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta ci gaba da samar da gudummawa tallafi ga 'yan gudun hijira daga kasashen waje bisa dokokin kasa da kasa da tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu. (Zainab)