Gigaba ya bayyana cewa, bisa sabuwar kididdigar da aka yi, an gano cewa ya zuwa ranar Litinin, baki 906 sun riga sun janye daga kasar Afirka ta Kudun bisa radin kan su.
An dai aiwatar da aikin debe irin wadannan baki 'yan kasashen ketare a wasu sansanoni dake dab da birnin Durban. Yawancin mutanen da suka bar kasar dai sun fito ne daga kasashen Zimbabwe, da kuma kasar Mozambique.
Kaza lika Gigaba ya kara da cewa alkaluman da aka samu ba su shafi ragowar sassa ba, kasancewar mai yiwuwa yawan bakin da suka bar kasar ya zarce hakan idan an hada da wadanda suka fita ta wasu hanyoyin na daban.
A daya hannun kuma, kungiyar likitoci marasa shinge ta fidda wata sanarwa dake cewa baki mazauna yankin Durban su 7400 sun rasa gidajensu a sakamakon barkewar rikicin, inda suke samun mafaka a sansanonin karbar 'yan gudun hijira 3. Tuni kuma kungiyar ta tura rukunin likitocin ta don samar da taimako ga 'yan gudun hijirar dake sansanin.
A wani ci gaban kuma, ministar tsaron kasar Afirka ta Kudu Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta bayyana cewa, kasarta ta tsaida kudurin tura sojoji zuwa yankunan da rikicin ya auku, don tabbatar da kwanciyar hankali cikin hanzari. (Zainab)