in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta Kudu ya nuna damuwa game da kisan 'yan sanda
2015-08-03 10:22:17 cri
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya nuna matukar damuwa game da yawaitar kisan 'yan sanda a sassan kasar sa.

Zuma wanda ya bayyana muhimmancin aikin 'yan sanda na kare doka, da kuma rayuka da dukiyoyin al'ummar kasa, ya yi tir da yadda ake samun bata gari masu hallaka 'yan sanda cikin 'yan makwannin baya bayan nan.

Ya ce ya zama wajibi al'ummar kasar su hada kai da jami'an tsaro wajen yaki da laifuffuka, domin cimma burin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar.

A cikin makon da ya gabata kadai, wasu bata gari sun hallaka 'yan sandan kasar 4, kana wasu 'yan fashi sun harbe wani dan sandan na daban a wani babban shagon sayar da kayayyaki dake birnin Johannesburg, lokacin da suke kokarin wawashe shagon.

Shugaba Zuma wanda ya yaba da kokarin jami'an tsaron kasar, ya yi kira gare su da su zage damtse wajen kare kawunan su daga harin miyagu, kamar yadda doka ta tanada.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa tsakanin shekarar bara da wannan shekara ta 2015, an hallaka 'yan sanda kimanin 86 a Afirka ta Kudu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China