in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron T20 ya mai da hankali kan tattalin arzikin kasar Sin
2015-09-07 13:47:56 cri

An kira taron dandalin tattaunawa tsakanin masana ilimin tattalin arziki na G20, taron da ya gudana tsakanin ranekun 3 zuwa 5 ga wata a birnin Ankara, fadar mulkin kasar Turkiyya, inda gungun mashawarta da masanan ilmin tattalin arziki na kasa da kasa suka tattauna makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, tare da nazari kan yadda kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na kasar da za ta shugabanci taron G20 a shekara mai zuwa.

A yayin taron T20, wato taron dandalin tattaunawa tsakanin masana a fannin ilimin tattalin arziki na kungiyar G20 na wannan karo, kwararru na kasa da kasa sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi karuwar tattalin arziki, da daidaita harkokin tattalin arzikin duniya, da kuma ajandar taron koli na G20. Kuma sakamakon yadda wasu kasashe ke gamuwa da tabarbarewar tattalin arziki, kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki su ma suna fuskantar kalubale, ana kuma tinkarar matsalar rashin tabbas ta fuskar tattalin arziki a duk duniya, wadda ta haddasa tangal-tangal ga kasuwar hada-hadar kudi, kana farashin kayayyaki ya ragu, baya ga darajar kudi ta wasu kasashe da ta yi matukar faduwa. Sakamakon wannan yanayi da ake ciki, tattalin arzikin kasar Sin ya yi matukar jawo hankulan masana.

Yanzu haka wasu kasashe sun fara nuna shakku kan tafiyar hawainiyar tattalin arzikin kasar Sin, da koma bayan kasuwarta ta takardun hada-hadar kudi, gami da batun tsarin tattalin arzikinta. Game da wannan, shugaban asusun nazarin manufofin tattalin arziki na kasar Turkiyya Guven Sak, yana ganin cewa hakan zuzuta halin da ake ciki ne kawai. Ya ce,

"A gani na, an zuzuta matsalar da tattalin arzikin kasar Sin ke fuskanta, musamman ma illar da batun tafiyar hawainiyar tattalin arzikin kasar ta haifar ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Ina so in dauki wani batu a matsayin misali, wato adadin kudaden da kasar Sin ta samu a fannin fitar da kayayyaki masu kunshe da sabbin fasahohin zamani zuwa ketare, ya kai kashi 5 zuwa 6 cikin kashi dari bisa dukkan adadin kudaden da Sin ta samu ta fuskar fitar da kayayyaki zuwa waje a shekarar 1990, amma yanzu wannan jimilla ta zarce kashi 25 cikin dari. A sa'i daya kuma, kasar Sin na kyautata matsayin musayar fasahohi. Hakan ya sa ana iya gano cewa, batun daidaita tsarin tattalin arzikin kasar Sin ya samu nasara."

A nasa bangaren kuma, Domenico Lombardi, mai kula da yanayin tattalin arzikin duniya na cibiyar kula da harkokin kirkire-kirkire na masanan kasar Canada, yana ganin cewa koma bayan kasuwar takardun hada-hadar kudin kasar Sin, ba ta nuni ga tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sin. Ya kara da cewa,

"kasar Sin kasa ce ta biyu mafi girma a duniya a fannin tattalin arziki. Tun bayan abkuwar matsalar tattalin arzikin duniya, ko da yaushe kasar Sin tana jagorantar ci gaban tattalin arzikin duniya. Ko da yake kasuwar takardun hada-hadar kudin kasar Sin ta samu tangarda, amma hakan ba ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya lalace."

Ban da shi, babban masani a fannin ilimin tattalin arziki na babban bankin kasar Turkiyya Yuksel Gormez, ya yi cikakken imani ga karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Inda ya furta cewa,

"A ganina, bai kamata a maida hankali ga yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a halin yanzu kawai ba, a maimakon haka ya kamata mu mai da hankali kan karuwar da za ta iya samu a nan gaba. Yanzu ba na iya ba da tabbaci kan cewar yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 10 cikin dari, amma idan kasar Sin na iya yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikinta yadda ya kamata, nan da shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa, to babu shakka yawan karuwar tattalin arzikinta za ta kai kashi 5 zuwa 10 cikin dari."

A yayin taron T20 na wannan karo kuma, kwararru da masana na kungiyar G20 sun ba da shawarwari kan ajandar taron kungiyar na shekarar 2016 wanda kasar Sin za ta jagoranta, inda Mr. Guven Sak, shugaban asusun nazarin manufofin tattalin arziki na kasar Turkiyya ya bayyana cewa, ana fatan kasar Sin za ta samar da muhimmiyar fa'ida a yayin taron G20 na shekarar 2016. Ya ce,

"Ina fatan za a iya kafa wani dandali don kanana da matsakaitan masana'antu bisa tsarin ajandar taron G20 na badi. Haka kuma ina fatan za a fadada mu'amala a tsakanin kasashe mambobin kungiyar, baya ga dora muhimmanci kan kasashen Afirka. Bugu da kari, game da matsalar bakin haure da ke tsananta yanzu, ya kamata a mai da hankali kan yadda za a kafa wani tsari na warware wannan matsala tun daga tushe."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China