in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata an nace ga matsayin raya tattalin arzikin duniya na bude kofa, in ji shugaban kasar Sin a taron koli na G20
2013-09-06 16:14:29 cri


An bude taron koli karo na 8 na kungiyar G20 a ran 5 ga wata a birnin Saint-Petersburg na kasar Rasha wanda aka yi masa lakabi da "Birnin da ke arewaci". Shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya halarci taron inda ya yi jawabi cewa, ya kamata a nace ga bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa. Ban da haka, Mr Xi ya nuna cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan zurfafa kwaskwarima a fannoni daban-daban, da kuma nace wa ga daukar matakin samun bunkasuwa tare da kawo moriyar juna. Sin na da karfi da ya dace wajen tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu, ana kasa warware matsalar tattalin arzikin duniya, kuma ana ci gaba da fuskantar matsalolin da illar hada-hadar kudi ta duniya ke haifarwa. Saboda haka, taron ya dauki jigon "Samun bunkasuwar tattalin arziki da samar da guraben aikin yi". A mataki na farko na taron, shugabanni mahalarta taron sun bayyana ra'ayinsu kan wasu manyan batutuwa ciki hadda halin tattalin arzikin duniya, ciniki, bunkasuwa, yi wa tsarin hada-hadar kudi na duniya kwaskwarima da dai sauransu. Mahalarta taro sun furta cewa, tattalin arzikin duniya bai samu cikakkiyar farfadowa ba, kuma yanzu ana fuskantar wani muhimmin lokaci, ya kamata, mambobin kasashen G20 su kara yin hadin gwiwa da sulhuntawa a fannin manufofi, kana masu ruwa da tsaki su daidaita matsaloli da tsarin manufofinsu na kudade da suke dauka, har ma da kiyaye dorewar kasuwar kudade ta duniya, sannan da mai da hankali kan moriyar kasashe daban-daban, ta yadda za a aza ginshiki mai kyau wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin dogon lokaci.

Wannan shi ne farko da shugaba Xi Jinping ya halarci irin wannan taro, kasancewar Sin kasa ta biyu a duniya mafi karfin tattalin arziki, yaya kasar Sin za ta shiga kokarin daidaita tattalin arzikin duniya? Kuma mene ne makomar tattalin arzikin kasar Sin? Duniya tana jiran ganin wane irin mataki Sin za ta dauka. A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya yi kira da a bunkasa tattalin arzikin duniya dake mai da hankali kan aikin kirkire-kirkire sannan da yin hadin gwiwa da samun moriya tare. Ya nuna cewa, raya sana'ar kirkire-kirkire na biyan bukatun samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa. Ya kamata, kasashe daban-daban su raya tattalin arzikinsu bisa matakai masu inganci, kuma su kara karfin takara a wannan fanni ta hanyar yi wa tsarinsu kwaskwarima. Samun bunkasuwa tare ya kasance bukata mai tushe wajen bunkasa tattalin arziki. Ya kamata, kasashe daban-daban su yi la'akari da moriyar sauran kasashe yayin da suke kokarin neman cimma moriyarsu. Ta yadda dukkan kasashe suka iya hada kansu wajen samun bunkasuwa tare yadda ya kamata. Kawo moriyar juna shi ne bukatun duniya na samun bunkasuwar tattalin arziki cikin daidaito. Ya kamata, kasashen duniya su kafa wani tsari mai kyau wajen samun bunkasuwa tare da kawo moriyar juna.

Shugaba Xi ya jadadda cewa, kafa irin wannan tsarin raya tattalin arzikin duniya yana bukatar mambobin kasashen G20 da su karfafa zumunci tsakaninsu tare da daukar nauyin dake wuyansu yadda ya kamata. Na farko, samar da manufar tattalin arziki mai amfani daga manyan fannoni. Sin na da karfin da ya dace wajen tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa, tare kuma da samarwa dukkan duniya zarafi mai yakini. Na biyu kuwa, yin hadin kai wajen tabbatar da raya tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa, tare kuma da yaki da manufar ba da kariya, da kuma kiyaye adalci da daidaici da manufar bude kofa da na hana nuna bambanci a fannin ciniki a duniya. Na uku kuma, kyautata tattalin arzikin duniya. Ya kamata, kasashe daban-daban su tabbatar da aikinsu a asusun IMF da manufar kwaskwarima da za su yi. Har ma da tsai da sabon tsari dake iya bayyana yawan kason da ko wace kasa za ta samu a duniya game da jimilar tattalin arziki.

Game da manufar da Sin take dauka a fannin tattalin arziki, Mr Xi ya nanata cewa, Sin tana nazari kan yadda za ta gudanar da aikin kwaskwarima a dukkan fannoni, ciki hadda tattalin arziki, siyasa, al'adu, al'umma, kiyaye muhalli. Yana mai cewa, Sin za ta kara karfin kafa tsarin kasuwanci, tare kuma da sa kaimi ga kwaskwarima da ake yi a fannin daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni, biyan haraji, hada-hadar kudi da sauransu, ta yadda za a yi amfani da tsarin kasuwanci yadda ya kamata a fannin rarraba albarkatun kasa. Sin za ta ci gaba da zurfafa yiwa kasuwar kudin ruwa da darajar kudi kwaskwarima, da kuma kyautata darajar kudin Sin a duniya. Sin za ta nace ga manufar hadin gwiwa da kawo moriyar juna, tare kuma da zurfafa kwaskwarima da take yi a fannin zuba jari da tsarin ciniki, har ma da daidaita manufofi a wannan fanni, domin samarwa kamfanonin kasashe daban-daban dake kasar Sin wani yanayi mai kyau, sannan kuma da daidaita wasu bambancin ra'ayi da ke akwai ta hanyar sulhuntawa.

An ce, za a ci gaba da mataki na biyu na taro a ran 6 ga wata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China