141118-G20APECCINHANC-Amina
|
Shugabannin dai sun kuduri aniyar yin hadin gwiwa a wannan fanni, tare da kafa wani tsari mai amfani, ta yadda za a kara taimakawa juna a fannin doka, da shari'a, da mai da wasu dukiyoyin da aka mallaka ba bisa ka'ida ba, da ma hana baiwa jami'ai da suka aikata laifuka masu alaka da hakan mafaka.
Tsarin da aka amince da shi ya nuna cewa, Sin ta fara hadin gwiwa da kasashen duniya masu yawa wajen yaki da cin hanci a dukkan fannoni.
Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na wakilan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekara ta 2012, aka mai da hankali sosai kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa, matakin da ya samu yabo kwarai daga jama'a. Ban da haka kuma, ana ganin cewa, wannan jigo ya zama muhimmin abu da aka tattauna yayin wasu manyan taruruka, ciki hadda na APEC da na kungiyar G20 da sauransu, wanda kuma ya nuna cewa, kasashe daban-daban na kara hadin gwiwa a wannan fanni. Direktan cibiyar nazarin hanyoyin gudanar da harkokin kasa yadda ya kamata ta Jami'ar Peking Mr. Li Chengyan ya bayyana cewa:
"Akwai ma'ana kwarai ga batun tattauna batun yaki da cin hanci da karbar rashawa, yayin wasu manyan taruruka da suka gudana, kamar na APEC da G20, tare da kafa wani tsari mai amfani. Matakin da ya bayyana cewa, Sin na kara hadin gwiwa da kasashen duniya a wannan fanni. Ta haka, kasashen duniya za su ba da taimako wajen cafke jami'an da suke aikata irin wannan laifi saboda rasa mafaka daga kasashe waje."
A matsayin muhimmin dandali na tattaunawa kan batun tattalin arziki, taron G20 ya dora muhimmanci kan batun yaki da cin hanci da karbar rashawa a shekarun da suka gabata, tare da kafa wani rukuni na musamman a wannan fanni, kana taron ya cimma wasu nasarori a fannin sa kaimi ga aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa, da nazari kan ayyukan yaki da cin hanci da kafa tsarin yaki da cin hanci da sauransu. Yawancin mambobin G20 ciki hadda kasar Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta MDD.
Game da hakan Mr. Li Chengyan ya ce:
"Wata muhimmiyar gwagwarmayya da muke yi a duniya wajen yaki da cin hanci ita ce batun mayar da dukiyoyin da wasu jami'ai suka yi rub da ciki a kan su zuwa kasashen su na ainihi, wadannan dukiyoyi sun hada da kudade masu dimbin yawa, wadanda ba za a iya mayar da su ba, sai da amincewar kasashe da dama, tare da sumun daidaito a fannin matsayin da suke dauka kan wannan batu karkashin jagorancin taron G20."
A ganin Mr. Li, ko da yake G20 za ta baiwa mambobinta taimako wajen yaki da cin hanci da karabar rashawa cikin shekaru biyu masu zuwa, a hannu guda akwai kalubale da mambobin za su iya fuskanta, wajen aiwatar da wadansu matakai dake da nasaba da wannan aiki. Ya ce:
"Shari'a da kuma tsarin siyasa iri-iri na kasashe daban daban, musamman ma bambancin tunani na gudanar da harkokin kasa, za su iya haifar da cikas ga hadin gwiwar da za a yi a wannan fanni, ba za a iya kauce wa hakan ba, ya kamata mu yi shiri tsaf domin gudanar da wannan aiki mataki-mataki. Ban da haka kuma, ya kamata mu lura da wani abu, wato kasashen yamma ba su canja wasu manufofin da suke kai game da yakin caccar baki, wato batun bada mafakar siyasa, matakin da mai yiwuwa ne ya kawo cika ga cafke, tare da tisa keyar irin wadancan jami'ai zuwa kasashensu. Dadin dadawa, ya kamata Sin ta kulla wasu yarjeniyoyi da kasashen duniya, ciki hadda Canada, da Austriliya da sauransu domin ba da tabbaci ga aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa cikin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban." (Amina)