in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron G20 a Brisbane zai mai da hankali kan tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya
2014-11-13 16:54:33 cri

Daga ranar 15 zuwa ta 16 ga watan Nuwamba ne, za a gudanar da taron shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20 a Brisbane na kasar Australiya.

Tun bayan da aka samu rikicin hada-hadar kudi a duniya a shekarar 2008, kungiyar G20 ta kasance wani muhimmin dandalin da kasashe masu karfin masana'antu da sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa suke musayar ra'ayoyi dangane da yanayin tattalin arzikin duniya. Kasashe 20 dake cikin wannan kungiya suke samar da kashi 75% na yawan kudin cinikin kasa da kasa, gami da kashi 85% na yawan kudin kayayyakin da ake samarwa a cikin gida na GDP na kasashen duniya.

Yanzu haka tattalin arzikin duniya na farfadowa, sai dai ci gaban da ake samu a wannan fanni ba shi da sauri. A bisa wannan yanayi ne, shugabannin kasashe mafi karfin tattalin arziki za su sake wata ganawa a Brisbane, 'yan kwanaki bayan da suka halarci taron kungiyar hadin kan tattalin arzikin Asiya da tekun Pasifik ta APEC da aka gudanar a nan birnin Beijing na kasar Sin.

Kasar Australiya a matsayinta na mai daukar bakuncin taron G20 na bana, ta sanya wani burin da za a cimma a taron wanda shi ne tabbatar da karuwar tattalin arzikin membobin kungiyar, kamar yadda Tony Abbott, firaministan kasar ya fada,

'Babban batun da za mu tattauna a wajen taron shi ne samar da wani tsarin tattalin arzikin duniya mai inganci, ganin yadda karuwar tattalin arziki za ta kara samar da guraben aikin yi, da zaman rayuwa mai inganci, sannan gwamnati za ta kara samun kudaden shiga da zai ba ta damar rage harajin da take karba, da samar da hidima mai kyau ga jama'a. Ya zuwa yanzu kasar Australiya ta sanya mambobin kungiyar G20 cimma ra'ayi daya, don kara daga matsayin tattalin arzikin kasar da kashi 2% bisa yadda aka yi hasashe a baya, cikin shekaru 5 masu zuwa.'

A shekarun baya, sannu a hankali taron G20 ya canza jigonsa daga tinkarar rikici zuwa neman samun karuwa mai dorewa. Haka kuma ana ganin alamun farfadowar tattalin arzikin duniya a bana, bisa la'akari da yadda karuwar tattalin arzikin kasar Amurka za ta iya kai kashi 3%, kana karuwar tattalin arzikin kasar Sin za ta iya tsayawa a kashi 7%, yayin da tattalin arzikin nahiyar Turai shi ma ya fara karuwa. Saboda haka, a cewar Ryan Manuel, wani mai nazarin kan yankin Asiya da tekun Pasifik dake jami'ar kasar Australiya ANU, za ga tasirin taron G20 ne a tsari na gaba.

"Nauyin dake wuyan kungiyar G20 shi ne tabbatar da tsarin da za a bi a nan gaba, don haka za a fi mai da hankali kan yadda za a samu ci gaban tattalin arzikim duniya mai dorewa, maimakon matakan daidaita matsalar da ake fama da ita yanzu sakamakon rikicin hada-hadar kudi."

Idan muka kalli taron G20 da ya gudana a birnin St. Petersburg na kasar Rasha a watan Satumba na bara, za mu ga yadda shugabannin kungiyar suka yi alkawarin tsara wani shirin raya tattalin arziki daga dukkan fannoni domin kara tattaunawa batun a taron Brisbane, shirin da aka ce zai shafi kara zuba jari, da samar da karin guraben aikin yi, da inganta cinikayya da takarar da ake yi, da dai sauransu. Kana a nata bangare, kasar Australiya ta zayyana wasu batutuwan da ke bukatar a fi lura da su a bana, wadanda suka hada da batun ciniki, samar da kayayyakin more rayuwa, biyan haraji, da harkokin banki. Dangane da haka, firaministan kasar Australiya Tony Abbott ya ce,

"Abubuwan da kungiyar G20 za ta fi mayar da hankali a kai su ne wasu muhimman bangarorin tattalin arziki, wato cinikayya, kayayyakin more rayuwa, harkokin haraji, da na banki. A wadannan fannoni za mu tattauna gibin kudi da ake fuskanta a duniya a fannin gina kayayyakin more rayuwa da ya kai dalar Amurka biliyan 1000, da magance matsalar biyan haraji, gami da kara baiwa jama'a damar shiga a dama da su a fannin neman guraben aikin yi."

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa bisa tsarin kungiyar G20 a kokarin tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya. Yayin da kasashen duniya suke kokarin fita daga cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki, a cewar Ryan Manuel, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa, amma kuma za ta fuskanci kalubale a fannin neman ci gaba mai dorewa kamar sauran kasashe. Don haka tattaunawar da za a yi za ta taimaka wajen kara fahimtar juna da tabbatar da samun ci gaba tare.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China