in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya kama hanyar halartar taron koli na G20
2014-11-14 16:03:15 cri

A yau Jumma'a 14 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga nan birnin Beijing, don fara ziyarar a wasu kasashen ketare. Kamar yadda aka tsara da farko zai halarci taron kolin kungiyar G20 da za a shirya a birnin Brisbane na kasar Australia, daga baya kuma zai kai ziyarar aiki a kasashen Australia, New Zealand, da kuma Fiji, inda kuma zai yi ganawa tare da shugabannin kasashen kananan tsibiran dake yankin Pasific da suka kulla huldar diplomasiyya da Sin. A jiya Alhamis 13 ga wata, wasu jami'ai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin suka bayar da sanarwa a yayin taron manema labaru cewa, halartar taron koli na G20 wani muhimmin matakin diplomasiyya na daban da shugaban kasar Sin zai dauka bayan da kasar Sin ta cimma nasarar shirya taron APEC.

Taron koli na kungiyar G20, wani muhimmin dandali ne da ake tattauna harkokin da suka shafi duniya, kuma wannan shi ne karo na biyu da shugaba Xi Jinping ya halarci taron. Shugaban sashen kula da harkokin tattalin arzikin kasa da kasa na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhang Jun ya bayyana cewa, halartar taron koli na G20 da shugaban kasar Sin zai yi wani muhimmin matakin diplomasiyya ne da kasar ta dauka, wanda kuma ke nuna cewa, kasar tana mai da hankali sosai kan kungiyar ta G20, tana kuma sauke nauyin dake kanta game da tattalin arzikin duniya.

"Shugaba Xi zai bayyana manufofin da kasar Sin ke dauka kan jerin batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arzikin duniya, yin kwaskwarima, harkokin cinikayya, samar da guraban aikin yi, makamashi da dai sauransu, kana zai gabatar da shawarar da Sin ta dauka kan wasu batutuwan, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban. Haka zalika shugaba Xi zai bayyana irin fasahohi masu kyau da Sin ta samu a yunkurin zurfafa yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, da kuma sabuwar dama da sabon karfi da tattalin arzikin kasar Sin ke samarwa a halin yanzu, domin yin kokari tare da sassa daban daban don inganta kungiyar G20 ta yadda za ta kara taka muhimmiyar rawa."

Game da taron kolin kungiyar G20 na wannan karo mai taken "bunkasuwar tattalin arziki, samar da guraban aikin yi, da tinkarar hadari", kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su iya bullo da sabbin matakai don inganta ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma hanzarta aiwatar da manufar asusun ba da lamuni na IMF game da harkokin kasa da kasa, ciki har da kara baiwa kasashe masu saurin ci gaba ikon bayyana ra'ayoyinsu, da karfafa hadin gwiwa a fannin makamashi da dai sauransu, ta yadda za a iya cimma sabbin ra'ayoyi guda kan kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai tsarin bude kofa. Bayan haka kuma, kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su mai da hankali kan mummunan tasirin da yaduwar cutar Ebola ke haifarwa tattalin arzikin duniya, ta yadda za su inganta hadin gwiwa a wannan fannin.

Abin lura a nan shi ne, za a sake tattauna batun hadin kai kan aikin yaki da cin hanci da rashawa a wannan babban taron duniya bayan taron APEC da aka kammala ba da dadewa ba a birnin Beijing na Sin. Shugaban sashen kula da harkokin tattalin arzikin duniya na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhang Jun ya bayyana cewa, a yayin wannan taron koli, ana sa ran karfafa hadin gwiwa a wadannan fannoni:

"za a karfafa hadin kai kan yadda za a yi farautar wadanda suka aikata laifuffuka da kudaden da aka samu ba bisa doka ba, da kuma mayar da kadarori.Tuni mambobi 21 na kungiyar APEC suka cimma matsaya daya kan wannan batun, ta yadda za a samu ci gaba a yayin taron G20, don haka muna sa ran ganin bullo da wani tsarin yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin duniya."

Bayan halartar taron koli na G20, shugaba Xi zai kai ziyarar aiki a kasashen Australia, New Zealand da kuma Fiji. Mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin, Zheng Guangze ya bayyana cewa, ziyarar na da ma'ana sosai wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da yankin Pasific.

"Shugaba Xi zai yi jawabi game da manufofi masu muhimmanci da kasar Sin ke bi game da yankin Pasific, zai kuma gabatar da jerin matakan da kasar ta dauka na nuna goyon baya ga bunkasuwar kasashen dake yankin, da kuma karfafa hadin kai tsakanin Sin da kasashen. Haza zalika a yayin ziyarar, shugaban zai sanya hannu kan wasu jerin takardun hadin kai tare da wasu kasashen yankin, wadanda za su shafi fannonin tattara kudi, ba da ilmi da horaswa, muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da dai sauransu." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China