in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta yi shiru a kan kiran ICC na cafke shugaban Sudan
2015-06-14 19:31:35 cri
Mahukuntan kasar Afirka ta Kudu a ranar Lahadi sun yi shiru bisa ga bukatun da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya da ta gabatar na kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da ke ziyarar aiki a kasar.

Kotun ta bukaci Afirka ta kudun da ta kama al-Bashir da zarar ya isa Jahannesburg domin halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 25.

An labarta cewa, al-Bashir ya isa Afirka ta kudu a Asabar da dare, amma duk da haka mahukuntan Afirka ta kudu ba su tabbatar da labarin ba.

Kotun na neman kama al-Bashir bisa zargin da take masa na laifuffukan keta hakkin dan Adam.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China