A tsawon shekaru biyar jere na baya bayan nan, kasar Sin ta rage jerin masu fitar da kayayyaki zuwa Afrika ta Kudu, in ji mista Langenhowen.
Nagartattun alkaluman da aka fitar sun nuna cewa musanya tsakanin kasar Sin da Afrika ta Kudu ta wuce dalar Amurka biliyan 220 a karon farko a cikin shekarar 2014, kuma kasar Sin ta kasance muhimmiyar abokiyar huldar kasuwancin Afrika a tsawon shekaru biyar da suka gabata.
Yanzu muna cikin wata matsala inda tarayyar Turai ta zama wani tsofon mutumin da ke fama da rashin lafiya domin tattalin arzikinsa na cikin raguwa, a cewar Langenhowen.
Masanin ya nuna cewa, karfin kasar Sin na a bayyane yanzu a cikin aikin sarrafa karafa inda take taimakawa da kashi biyu cikin kashi uku na karfin duniya a wannan fannin.
Amma kuma duk da haka, ya bayyana cewa, akwai wasu kalubalolin da ya kamata Afrika ta Kudu ta fuskanta domin ganin shirin farfado da masana'antu na samu nasara.
Martin Solomon, mataimakin shugaba na farko na kamfanin Sasol Limited, na goyon bayan wannan ra'ayi, tare da bayyana cewa wadanda ke shirin zuba jari a Afrika, musammun ma a Afrika ta Kudu, suna bukatar su fara cikin gaggawa.
Afrika na da arzikin man fetur sosai. Nahiyar Afrika na tattare da ruwan samar da wutar lantarki, lamarin da zai kawo wani yunkuri ga masu neman zuba jari. Masana'antun man fetur da na gas su ma suna damammaki masu tarin yawa, in ji mista Solomon. (Maman Ada)