Wannan dalilin ya sa muka dauki niyya, a matsayinmu shugabanni, cewa bai kamata mu ci gaba da sarrafa albarkatun ma'adinanmu a wajen nahiyar Afrika ba, dukkan albarkatunmu ya kamata a ce ana sarrafa su a nan Afrika ta yadda al'ummomin kasashen Afrika za su samu moriya, in ji shugaba Zuma a yayin taron kungiyar Afrika karo na 25 da ke gudana a birnin Jonhannesburg.
Zuma ya yi wannan kira a yayin da yake halartar wani taron "babban aiki na shugabancin kungiyar AU" wanda burinsa shi ne tattara kudade domin gidauniyyar tarayyar Afrika.
Zuma ya karbi bakuncin dukkan shugabanni da gwamnatoci har ma da tawagogi daban daban a wannan dandali na tarihi, tare da bayyana cewa Afrika ta Kudu, na farin ciki da karramawar da aka mata na karbar jagoranci na nahiyarmu domin wannan muhimmin dandali.
Dandalin na gudana a cibiyar yarjejeniyar kasa da kasa ta Sandton da ke birnin Johannesburg bisa taken: Shekarar wayin kan mata da bunkasuwa game da ajandar shekarar 2063 na Afrika". (Maman Ada)