Mr Ban dai ya zo birnin Beijing ne domin halartar bikin cika shekaru 70 da kasar Sin ta samu nasara a kan mayakan Japan da kuma karshen yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo wato fascist.
Firaministan na kasar Sin ya ce wannan shekarear ta zo daidai da cika shekaru 70 na kafa MDD kuma majalissar ta taka rawar a zo a gani wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta ci gaba ga kowane bangare.
Ya ce Sin na fatan kara matsin lamba na ganin an cimma amincewa a batutuwan da majalissar ta tsara a babban taronta na bara, tare da kiyaye ci gaban da aka samu na yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo da kuma dokar da aka samar bayan yakin duniya na biyu.
Haka kuma Li Keqiang ya tabbatar da cewa kasar Sin za ta ci gaba da inganta zaman lafiya a duniya baki daya da kuma tabbatar da dorewar shi domin cimma sabon ci gaba da kuma sabbin dabaru.
Har ila yau Firaminista Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da ba da karfi a ayyukan kawar da talauci, za ta kuma yi kokarin matuka wajen magance matsalar sauyin yanayi da kuma ba da gudunmawa mai nagarta a aiwatar da ayyukan muradan majalissar bayan shekara ta 2015. (Fatimah Jibril)