Firaminista Li ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar gudanarwar kasar Sin na musamman da ya gudana a Zhongnanhai, inda gwamnatin tsakiyar kasar Sin take don tattauna ci gaban da aka samu a duniya a bangaren tattalin arziki da harkokin kudi da kuma illolinsu ga kasar ta Sin kana da matakan da suka dace a dauka.
Ya ce, duk da canje-canje masu sarkakiya da ake fuskanta a ketare da wasu manyan matsalolin cikin gida, hakan bai hana tattalin arzkin kasar samun ci gaba ba. Ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnati za ta kara daukar matakai don ganin an samu dorewar ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma matakan yin gyare-gyaren da ake aiwatarwa.
Mr Li ya kuma bayyana cewa, nuna fifikon da ake samu a kasuwannin duniya na baya-bayan nan, ya kara haifar da rashin tabbas game da farfadowar tattalin arzikin duniya, wadda hakan ke haifar da illa ga kasuwannin hada-hadar kudin kasar da kayayyakin da ke shigawar da fitarwa. Kuma wadannan wasu karin matsin lamba ne ga tattalin arzikin kasar.
Firaminisdta Li ya ce, gwamnati ta dauki sabbin matakan zurfafa yin gyare-gyare da bunkasuwa ne ta nufin kara karfin ci gaban tattalin arzkin kasar tare da daidaita harkokin kasuwannin kasar kamar yadda ake fata. (Ibrahim Yaya)