Da yammacin yau ne, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya gana da mista K.V. Kamath, gwamnan farko na bankin raya kasa na BRICS da 'yan rakiyarsa a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, mista Li ya ce, kafa bankin na BRICS, wata alama ce da ke nuna cewa, kasashen BRICS sun dauki muhimmin mataki na kyautata hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Kana wani muhimmin mataki ne ta fuskar yin hadin gwiwar kudi a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma kasashe masu saurin bunkasa ta fuskar tattalin arziki, sa'an nan bankin zai taimaka wajen kyautata tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa.
Kasar Sin na son yin kokari da sauran mambobin kungiyar wajen ganin an kyautata yadda ake tafiyar da harkar bankin, a kokarin raya bankin ta yadda zai dace da zamani
A nasa bangaren, mista Kamath ya yaba wa kokarin kasar Sin wajen raya kasa, karfin hali dangane da hanyar da kasar Sin ke bi wajen raya tattalin arziki da makomarta ta samun bunkasuwa mai dorewa da kuma yadda take raya kasuwar hada-hadar kudi. Bankin raya kasa na BRICS zai yi bullo da sabuwar hanyar amfani da karfi da kwarewar da kasashen BRICS suke da shi ta fuskar bunkasa tattalin arziki da kuma hada kai wajen kera kayayyaki, a kokarin samun bunkasuwa tare. (Tasallah Yuan)