Shekau ya kuma karyata ikirarin da sojojin Najeriya suka yi cikin faifan na tsawon mituna takwas cikin harshen Hausa cewa, sun kashe shi kuma an maye gurbinsa a matsayin shugaban kungiyar.
Tun a watan Maris rabon a ga Shekau din a faya-fayen bidiyon da kungiyar ta Boko Haram da saba fitarwa, batun da ya haifar da shakkun cewa, watakila an kashe shi ko kuma wasu sun maye gurbinsa. (Ibrahim)