in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karshen aikin tawagar MDD ta yaki da Ebola: WHO zata kama hannu a ranar 1 ga watan Augusta
2015-08-01 14:21:17 cri
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya sanar a ranar Jumma'a da kawo karshen aikin tawagar yaki da cutar Ebola ta MDD (MINUAUCE) a jiya ranar 31 ga watan Julin shekarar 2015, tare da jaddada cewa MDD zata cigaba da kokarinta wajen yaki da annobar a karkashin jagorancin hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO).

Mista Ban ya kara da cewa, tun daga wannan rana daya ga watan Augusta, nauyin aikin yaki da cutar Ebola na MDD zai koma hannun kungiyar WHO baki daya, a karkashin ikon darekta janar ta hukumar, dokta Margaret Chan.

A shirye nike sosai wajen kara daidaita babban matsayin niyyar MDD yadda ya kamata domin kai ga samun nasarar babu mutum guda mai dauke da cutar Ebola, in ji mista Ban, tare da jaddada cewa ma'aikatan da a yanzu haka suke kula da aikin tawagar zasu cigaba da tsayawa a kan aiki a wurin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China