Wata sanarwar da rundunan sojojin kasar ta fitar ta bayyana cewa, an damke kwamandan kungiyar da ba a bayyana sunansa ba a wani samame da ta kaddamar a karshen makon da ya gabata a wata maboyar 'yan ta'addan da ke Aulari a yankin Bama da ke jihar ta Borno.
Kakakin runduna ta 7 ta sojojin Najeriya Kanar Tukur Gusau ya bayyana cewa, dakarun sun kuma yi nasarar tarwatsa sansanonin mayakan a sama da kauyuka 9 da ke yankin da ke fama da rikicin na Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram dai ta halaka mutane sama da 13,000 kana da dama sun jikatta a hare-haren da ta kaddamar a cikin shekaru 6 da suka gabata.
Kungiyar ta kuma zafafa hare-haren da take kaddamarwa a arewa maso gabashin Najeriya, tun lokacin da aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a watan Mayun wannan shekara, inda ya lashi takwabin kawar da kungiyar. (Ibrahim)