A ranar 3 ga watan Satumba, kasar Sin za ta yi faretin soja domin tunawa da ranar cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan. Masani kan kayayyakin aikin soja, kana mataimakin farfesa dake aiki a jami'ar tsaron kasa ta Sin, Ge Lide ya bayyana cewa, faretin soja da za a yi zai gwada makaman da sojojin kasar Sin suke amfani da su, ciki har da wasu sabbin makamai, wadanda za su bayyana babban sakamako da aka samu wajen bunkasa makaman rundunar sojojin Sin. Ban da haka, a cewar Li Guangbin, wani hafsan dake aiki a hadaddiyar hukumar ba da umurni kan faretin sojan, sabbin makamai da kayayyakin da za a nuna a faretin soja da dama sun riga sun kai matsayin ci gaba a duniya.
Mista Ge Lide ya kara da cewa, a gun faretin soja, sabbin jiragen saman yaki da suke iya tasowa daga kan jirgin ruwa za su fi jawo hankula. Saboda su za su bayyana karfin babban jirgin ruwan yaki na kasar Sin.(Fatima)