in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi karin bayani kan yadda za ta yi faretin soja a ranar 3 ga watan Satumba
2015-08-21 19:07:02 cri

Yau Jumma'a 21 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira taron manema labaru, inda ya yi karin bayani kan yadda za a yi faretin soja a ranar 3 ga watan Satumban bana domin murnar cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu, da kuma nasarar da Sinawa suka samu kan mayakan Japan.

Mutane dubu 12 za su shiga wannan faretin soja, yayin da za a yi amfani da na'urori na nau'o'i fiye da 40 wadanda yawansu ya wuce dari 5, sa'an nan za a yi amfani da jiragen sama na nau'o'i fiye da 20, wadanda yawansu ya kai kusan dari 2. Akwai rukunoni 50 a cikin faretin sojan bana, tare da yin nune-nunen makamai da na'urori kirar kasar Sin, wadanda kashi 84 cikin dari ne daga cikinsu karo na farko ne za a gwada su a fili.

Ya zuwa yanzu kasashe fiye da 10 kamar Rasha, Kazakhstan, za su aika da sojinsu ko tawagoginsu shiga faretin sojan. Sojoji da tawagogi na kasashen waje sun fito ne daga kasashen Asiya, Turai, Afirke, Oceania da Amurka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China