A yayin ziyarar, ana sa ran jama'a za su kalli jiragen ruwan yakin, inda za a shirya liyafa a kan jirgaren ruwan, da ziyartar gidan marayu, shirya gasar wasan kwallon kafa tare da sojojin ruwa na Sudan da dai sauransu.
Mashigin tekun Sudan yana arewa maso gabashin kasar ne, wanda shi ne hanyar cinikayyar kasashen waje daya tilo ga kasar ta Sudan, kuma ana kiran mashigin da suna "mashigar kasar Sudan". (Zainab)