Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ya ce, akwai yiwuwar cimma matsaya game da batun nukiliyar kasar Iran nan da wa'adin karshe na tattaunawar da ake gudanarwa a Vienna.
Kerry wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, bayan ganawarsa da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif, ya ce, daukacin sassan da wannan batu ya shafa na mai da hankali game da tattaunawar da ake gudanarwa, kuma a cewar sa, Amurka na daukar dukkanin matakan da suka wajaba na ganin an cimma wannan nasara.
Sakataren wajen na Amurka ya shaidawa manema labaru cewa, lokaci ya yi, da za a zage damtse domin ganin an kai ga cimma yarjejeniya tsakanin masu tattaunawar.
Sai dai duk da wannan hasashe na Kerry, a hannu guda ya ce, kawo wannan lokaci ba a kai ga warware wasu daga muhimman batutuwa masu sarkakiya da suka shafi shawarwarin ba. Ya ce, ya amince da kalaman wakilin kasar Iran, cewa Iran din da sauran kasahen dake tattaunawa game da nukuliyar ta, a wannan karo na kusa da cimma matsaya, sama da matsayin da suka kai a lokutan baya.
A daya hannun kuma, Kerry ya ce, burinsu a wannan karo shi ne cimma cikakkiyar yarjejeniya ba tare da kauce-kauce ba.
Gabanin kalaman na Kerry dai wakilin kasar Iran Javad Zarif, ya fidda wani sako wanda aka wallafa ta shafukan yanar gizo na YouTube, inda yake cewa, duk da sabanin dake akwai tsakanin sassan dake tattaunawar a wannan karo, a wannan lokaci an samu ci gaba sama da na sauran lokutan baya.
A baya dai sassan dake tattauanwar sun gaza cimma matsaya gabanin wa'adin 30 ga watan Yunin da ya gabata, lamarin da ya sanya tsawaita wa'adin zuwa 7 ga watan Yulin nan. Idan dai an cimma matsaya a wannan karo, hakan zai sanya Iran din dakatar da wasu daga ayyukan ta na sarrafa nukiliya, yayin da hakan zai sanya kasashen yamma dage wasu daga takunkumin da suka kakaba mata. (Saminu)