Har zuwa daren jiya Lahadi, ba a cimma matsaya daya kan yarjejeniya ta karshe daga dukkan fannoni ba a gun taron shawarwarin nukiliya na Iran da ake yi a birnin Vienna. A wannan rana, ministan harkokin waje da wakilan kasashe 6 da batun nukiliya na Iran ya shafa sun yi shawarwari sau da dama, domin kawar da sabane-sabanen dake kasancewa a tsakaninsu. Ya zuwa yanzu, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi shi ma ya isa birnin don yin shawarwarin.
Ko da yake an jinkirtar da lokacin yin shawarwarin nukiliya sau da dama, amma ana kusan cimma nasarar kulla wata yarjejeniya ta karshe. Ko da yake 12 ga wata, ranar Lahadi ce, amma ba a daina yin shawarwari ba, ayyukan da ministan harkokin waje na kasashe 6 suka yi sun jawo hankalin mutane sosai. A kwanan baya, ministocin harkokin waje na kasashen Jamus da Faransa da Ingila sun tafi birnin Vienna sau da dama. A wannan rana da yamma, ministan harkokin waje na kasar Rasha Lavrov da kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi sun isa birnin. Ana sa ran za a cimma nasarar kulla yarjejeniya dalilin isowar ministocin harkokin waje na kashen Rasha da Sin.
A jiya Lahadi kuwa, an ci gaba da yin shawarwari a tsakanin bangarori biyu, kuma an fayyace cewa, bangarori daban daban suna da banbancin ra'ayi kan wasu muhimman batutuwan dake cikin yarjejeniyar, amma sun bayyana cewa, za a cimma matsaya daya kan wadannan batutuwan. A halin yanzu, bangarori daban daban suna kokarin kawar da sabani domin kammala rubuta dukkan takardu. An kuma ba da labari cewa, za a sanar da cimma matsaya daya kan yarjejeniyar a kwananki masu zuwa.(Lami)