in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya kalubalanci majalisar dokokin kasar da ta zartas da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma
2015-07-16 14:01:36 cri

A jiya Laraba, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kalubalanci majalisar dokokin kasar da ta zartas da yarjejeniyar da aka cimma game da nukiliyar Iran a dukkan fannoni, kuma wannan yarjejeniya ita ce hanya mafi kyau ta hana karuwar makaman nukiliya da yake-yake a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mr. Obama ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a fadar White House a wannan rana cewa, cimma wannan yarjejeniya ita ce hanya mafi kyau ta hana kasar Iran samun makaman nukiliya, in ba haka ba, sauran kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya su ma za su yi kokarin mallakar makaman nukiliya.

Da zarar cimma wannan yarjejeniya, sai ta samu adawa daga 'yan jam'iyyar demokarat a majalisar dokokin Amurka da kuma kasar Isra'ila.

A jawabin da ya gabatar a ranar talata game da wannan yarjejeniya, shugaba Obama ya ce, wannan yarjejeniya ta dace da abubuwan da aka tattauna a gun shawarwarin kasashen nan 6 da kasar Iran a watan Afrilu, ya kuma tabbatar da cewa, ta dace da muradun kasar Amurka da kuma kawayenta ta fuskar tsaro.

Majalisar dokokin kasar Amurka za ta nazarci wannan yarjejeniya kana ta jefa kuri'a cikin kwanaki 60 masu zuwa. Mr. Obama ya yi gargadin cewa, a shirye yake ya hau kujerar naki idan har 'yan majalisar suka yi kokarin kin amincewa da wannan yarjejeniya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China