Kasar Najeriya za ta cigaba da goyon bayan yin amfani da fasahar nukiliya, amma kawai bisa moriyar zaman lafiya da kuma bunkasa ci gaban jama'a, in ji shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis.
Shugaban Najeriya ya yi wadannan kalamai a lokacin da yake karbar mataimakin shugaban Iran kan harkokin waje, Mohammed Shariatmadari, da ke ziyarar aiki a Abuja, babban birnin Najeriya, ya kuma bayyana cewa, kasarsa dake yammacin Afrika ta yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma a wannan mako tsakanin Iran da manyan kasashe shida kan shirin nukiliya na Iran.
Shugaba Buhari ya kimanta wannan yarjejeniya da wani abin alheri, da kasancewa babban ci gaba domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.
A matsayin wata kasar da ta rattaba hannu kan kudurin hana yaduwar makaman nukiliya daga dukkan fannoni, Najeriya na aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin da abin ya shafa suka cimma, in ji shugaban kasar.
Mataimakin shugaban kasar Iran, da ke ziyara a Najeriya, ya mika wa shugaba Buhari goyon gayyata domin halarta taron kasashen da ke fitar da gas da za a shirya a birnin Teheran. Haka kuma ya yi alkawarin tallafin kasarsa ga Najeriya da ke yaki da kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)