Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada fatan da kasar ke da shi na alheri wajen ganin ci gaban dangantaka tsakaninta da Amurka, a lokacin da ya gana da mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasar Amurka Susan Rice.
Madam Rice dai ta iso nan birnin Beijing ne domin share fage na ziyarar da Shugaba Xi zai kai kasar ta Amurka a watan gobe tare da ganawa da shugaban kasar Barrack Obama a watan gobe na Satumba.
Shugaba Xi ya ce Sin da Amurka ya kamata su azalzala tattaunawa a kan yarjejeniyar zuba jari da kuma fadada sadarwa a tsakanin sojojinsu. Yana mai lura cewa kasashen biyu har ila yau ya kamata su kara neman karin hadin gwiwwa a bangaren makamashi da kayayyakin more rayuwa da kuma sauran batutuwan da suka shafi duniya kamar sauyin yanayi da batun yankin Asiya da Fasific.
Har ila yau Shugaban kasar na Sin ya kuma jaddada muhimmancin daidaita da banbancin dake tsakanin kasashen biyu tare da mutunta ra'ayin junansu.
A nata bangaren Susan Rice ta ce shugaba Obama yana zura ido na ziyarar shugaba Xi yana kuma fatan ganin karin hadin gwiwwa ya wanzu a tsakanin kasashen biyu.
Kafin ganawar dai da Shugaba Xi , sai da Madam Susan Rice ta gana da kansilar majalisar gudanarwa ta gwamnatin kasar Sin Yang Jiechi, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da kuma janar Fan Changlong mataimakin shugaban kwamitin sojojin tsakiya na kasar Sin. (Fatimah JIbril)