Shugaba Xi ya yi wadannan kalamai ne yayin taron babban kwamitin kula da yin gyare-gyare na kasa karo na 15.
Tun lokacin da aka fara zurfafa yin gyare-gyare a sassa daban-daban na kasar, aka fara ganin kyakkyawan sakamako a farkon wannan shekara.
Don haka ya jaddada cewa, wajibi ne bangaren JKS da gwamnati a dukkan matakai su kara zage damtse da nuna juriya wajen kara zurfafa yin gyare-gyare, tare da fito da matakan magance sabbin matsalolin da suka kunno kai yayin da ake aiwatar da wadannan gyare-gyare.
A karshen shekarar 2013 ne aka kafa wannan kwamiti domin sa-ido kan yadda shirin zurfafa yin gyare-gyaren ke gudana.
Taron na yau Talata ya samu halartar manyan shugabannin da suka hada da firaminista Li Keqiang, Liu Yunshan da kuma mataimatin firaminista Zhang Gaoli. (Ibrahim)