in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tarihi kan harkokin kimiyya na kasa da kasa a birnin Jinan
2015-08-24 10:02:41 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kiran da a kara mayar da hankali kan nazarin da ya shafi harkokin tarihi, ta yadda za a samar da makoma mai haske a nan gaba.

Shugaba Xi ya yi wannan kiran ne cikin sakon da ya aike ga taron tarihin harkokin kimiyya na kasa da kasa da aka bude jiya Lahadi a birnin Jinan da ke lardin Shandong.

Ya ce, tarihi shi ne tushen duk wani nazarin rayuwar bil-Adam, kana wata kafa ce ta fahimtar abubuwa da suka faru a baya, sanin abin da ke faruwa a yanzu, da kuma tsara abin da ka iya kasancewa a nan gaba.

Shugaba Xi ya kara da cewa, ko wace kasa tana da tsarinta na bunkasuwa, don haka kamata ya yi kasashe su martaba zabin sauran kasashe. Kuma zurfafa moriyar juna zai taimaka wajen inganta rayuwa a nan gaba.

Wannan shi ne karon farko da aka shirya wannan taro a wata kasar Asiya, tun lokacin da aka fara shi a shekarar 1900.

Sama da wakilai 2,600 daga kasashe da shiyyoyi 90 ne ke halartar taron da ake gudanarwa bayan shekaru biyar-biyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China