A tsawon rangadin aikisa na sanya ido a Jilin daga ranar Alhamis zuwa Asabar, mista Xi ya isa Yanbian, da ke tattare da kabilar Koriya mafi girma ta kasar da kuma cibiyar yankin cigaba na Changchun-Jilin-Tumen.
Wannan yanki na da babban muhimmanci ta fuskar bude kofar yankunan dake kan iyakoki da kuma dangantakar kasa da kasa a yankin Asiya dake arewa maso gabashi, in ji mista Xi Jinping.
Haka kuma wannan yankin gwaji na da muhimmiyar ma'ana wajen daidaita tattalin arziki a arewa maso gabashin kasar Sin, wanda ya kasance wani muhimmin tushe na manyan kamfanonin kere kere amma ya fuskanci matsala dalilin ja da bayan tattalin arziki a 'yan shekarun baya bayan nan, in ji shugaban kasar Sin tare da yin kira ga shugabannin wannan yanki da su tsara shiri cikin taka tsantsan bisa ci gaban wurin, da su amfani da albarkatun wurin domin kara karfi da inganci, da mayar da yankin a matsayin wani misalin bude kofa a arewa maso gabashi. Bayan ya ziyarci yankin ci gaba, mista Xi ya kuma je wani karamin kauye dake yankin Yanbian domin yin hira tare da manoma. Bisa jaddada mahimmancin tsaron abinci a cikin kasar, shugaban kasar Sin ya yi alkawarin kara samar da tallafi ga yankunan noma domin tattalin arzikin wurin ya kyautatu kuma manoma su kara samun kudin shigarsu sakamakon ci gaban noma. (Maman Ada)