in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya jaddada bukatar kara karfin sojoji daga tushe
2015-07-20 09:54:04 cri
A jajebirin bikin kafuwar rundunar sojojin kasar Sin, shugaba Xi Jinping na kasar ta Sin, ya yi rangadi zuwa rukuni na 16 na sojojin kasar Sin, inda a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kwamitin soji na tsakiya, ya mika sakon gaisuwar musamman ga daukacin sojoji dake aiki a rukunin, da ma daukacin sauran kwamandojin sojoji da na sojojin ko-ta-kwana, bisa zagayowar wannan biki mai muhimmanci.

Bayan sauraron rahoton aiki da wakilan sojojin suka gabatar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya zama dole a nace ga bin manufar horar da sojoji sabbin tunani, da karfafa zukatansu wajen kara bautawa jama'a, kana a ko da yaushe ya wajaba sojojin su zamo masu bin umurnin jam'iyya, da bin ka'idojin kwamitin tsakiya, da na kwamitin soji na tsakiya.

Xi Jinping ya ce, ya zama wajibi a fadakar da sojoji muhimmnacin bin dokoki da ka'idoji, don kara kwarewarsu. Kaza lika, ya kamata a mai da hankali game da wahalhalun da sojojin ke fuskanta, da tabbatar da hakkinsu, don kara bunkasa kwazon su.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China