in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Turkiyya
2015-07-30 10:12:59 cri
A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a nan birnin Beijing da yanzu haka yake ziyarar aiki a nan kasar. Shugabannin sun bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su tabbatar da makomar dangantakar kasashen biyu, don kara amincewar juna a fannin siyasa, da nunawa juna goyon baya game da muhimman batutuwan da aka dora muhimmanci sosai a kansu, ta yadda za a hada dabarun raya kasashen biyu tare, da inganta dangantakar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, Sin da Turkiyya, muhimman mambobin kungiyar G20 ne, bisa ga sauye-sauyen da duniya ke fuskanta da tafiyar hawainiya wajen farfadowar tattalin arzikin duniya, da yadda ayyukan ta'addanci ke kara kamari a yankunan yammacin Asiya da arewacin Afrika, kalubale da kasashen biyu ke fuskanta da alhakin da ke wuyansu sun kara karuwa, don haka ya zama dole bangarorin biyu su karfafa amincewa da juna, da inganta dangantakar sada zumunta a tsakaninsu. Shugaba Erdogan da gwamnatin Turkiyya sun sha nanata kudurinsu na yaki da aika-aikar da ke kawo barna ga mulki da cikakken yankin kasar, da yaki da ayyukan ta'addanci. Kasar Sin ta yabawa wannan mataki, tana kuma fatan inganta hadin gwiwa a fannin tsaro a tsakaninsu. Har kullum kasar Sin tana goyon bayan hukumomin tsara dokokin da gwamnatocin kasashen biyu su kara mu'amala, don inganta shawarwari game da manufofi da matakan kara amincewar juna a fannin siyasa, don tabbatar da cewa, dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu ta kama hanya yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaba Erdogan ya ce, har kullum gwamnatin Turkiyya ta dora muhimmanci sosai game da raya alakar dake tsakaninta da Sin, kuma za ta dukufa ka'in da na'in don raya dangantakar hadin gwiwar da ke tsakaninsu. A yayin da sassan biyu ke murnar cika shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, kasar Turkiyya na fatan yin kokari tare da Sin, don fadada hanyoyin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da cinikayya da zuba jari da kimiyya da fasaha, da gina muhimman ababen more rayuwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China