in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha tare da kasar Nijar
2015-08-28 11:06:57 cri

Ministar harkokin wajen kasar Nijar Aichatou Mindaoudou, ta sa sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha tare da jakadan kasar Sin dake Jamhuriyar Nijar Shi Hu, a madadin gwamnatocin kasashen biyu a birnin Niamey a ranar 26 ga wata.

Game da hakan, Mindaoudou ta bayyana cewa, kasar Sin ta samar da tallafi da dama ga kasar Nijar a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa, da na jiyya da fannin ilimi. Ministar wadda ke tsokaci a gun bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a Laraba, ta ce hakan ya kara azama sosai ga ci gaban zamantakewar al'ummar Nijar.

Ta kuma yi imanin cewa, kulla wannan yarjejeniya zai ba da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin kasar Nijar, wajen tabbatar da shirin farfado da kasar cikin lokaci. A madadin shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, da gwamnatin kasar, ministar ta jinjinawa taimakon da kasar Sin ke baiwa kasarta.

A nasa bangare, jakada Shi Hu ya bayyana cewa, kulla wannan yarjejeniya ya zama wani muhimmin batu a fannin hadin gwiwar kasashen Sin da Nijar, ya kuma shaida dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, tare da bayyana goyon baya ga gwamnatin Sin ke nunawa kasar Nijar a kokarinta na neman samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Ya kara da cewa gwamnatin Sin, za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa a tsakaninta da Nijar, da nufin cimma moriyar juna.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China