in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bom da aka kai a arewa maso gabashin Nijeriya ya haddasa mutuwar mutane 11
2015-05-15 10:41:53 cri
Harin kunar-bakin-wake da aka kai a daren shekaranjiya Laraba 13 ga wata a birnin Maiduguri na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Sojojin kasar da suka tabbatar da wannan labari, sun bayyana cewa, wata mata ce, ta kai harin kunar-bakin-wake da aka dana a jikinta a wani sansanin dake kusa da Maiduguri, abun da ya haddasa mutuwar sojoji kimanin 11. Bayan da bam din ya fashe, sojojin Nijeriya sun isa wurin tare da yi kangiya.

Wani sojin da ya bukaci a sakaya sunan shi, ya ce, a kwanakin nan, sojoji sun kara karfi wajen yaki da kungiyar Boko-Haram, abin da ya sa 'yan ta'adda su ma suka fara yin amfani da mata don kai harin kunar-bakin-wake, hakan ya sa sansanonin sojoji suke yawan samun harin daga 'yan ta'adda.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China