in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bankin raya kasar Najeriya
2015-03-24 10:33:10 cri

Bankin raya tarayyar Najeriya da aka bude a jiya Litinin a birnin Lagos zai gyara kanana, da kuma matsakaitan kamfanonin kasar.

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya gabatar a bikin kaddamar da bankin. Shugaban ya kuma yi fatan cewa, bankin zai kawar da shinge ga kanana da kuma matsakaitan kamfanoni, ta yadda zai ba da damar samar da karin ayyukan yi a kasar.

Ya ce, bankin raya kasa wata cibiyar cinikayya ce mai zaman kanta, wadda ke iya sassauta matsin lambar da kanana, da matsakaitan masana'antu ke fuskanta, wajen neman samun bunkasuwa mai dorewa.

Ya kara da cewa, ya kamata bankin ya gudanar da ayyuka bisa ka'idojin cinikayya, ta hanya mafi kyau da ake amfani da ita a duniya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China