Sanarwar ta bayyana cewa, a ganin Ban Ki-moon, yadda aka cimma nasara a kokarin gudanar da zaben shugaban kasar Nijeriya ya shaida cewa, ana bin tsarin demokradiyya a kasar, kuma yana fatan za a ci gaba da bin wannan tunanin a zaben gwamnonin jihohin da na 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a ranar 11 ga wata.
sanarwar har ila yau ta ce, Ban Ki-moon ya yaba ma shugaban kasar na yanzu Goodluck Jonathan da ya jagoranci dukkan ayyukan zaben shugaban kasar a wannan karo da kare ra'ayin demokradiyya. Daga nan sai ya yi kira ga dukkan jama'ar kasar Nijeriya da su amince da sakamakon zaben. A cewar mista Ban, idan akwai shakka, kamata ya yi a warware ta ta hanyar dokokin kasar. (Zainab)