Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa kasar sa da nahiyar Afirka suna da moriya ta bai daya. Kuma daya daga cikin manyan manufofin kasar Sin ita ce kokarin karfafa huldar hadin gwiwa tare da kasashen Afirka.
Shugaba Xi ya yi fatan ci gaba da kokari tare da kasashen Afirka, wajen yaukaka abokantakar dake tsakaninsu, tare da sa kaimi ga bunkasa hadin gwiwar su, don tabbatar da moriyar juna da samun ci gaba tare.
A na sa bangare, shugaba Zuma jinjinawa goyon bayan da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka ya yi a kokarinsu na raya tattalin arziki, da yadda kasar Sin ke lura da matsayin kasashen Afirka dangane da manyan batutuwan kasa da kasa, da ma yadda kasar take daukar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da muhimmancin gaske. (Bello Wang)