in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala wani sabon zagayen shawarwarin siyasa a tsakanin 'yan kasar Libiya
2015-08-13 10:13:41 cri
Wani sabon zagayen shawarwarin siyasa a tsakanin 'yan kasar Libiya da aka bude a ranar Talata a karkashin jagorancin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libiya (MANUL) ya kammala a ranar Laraba a birnin Geneva bayan kwanaki biyu ana tattaunawa.

Shawarwarin, da manzon musammun na MDD dake kasar Libiya, mista Bernardino Leon ya jagoranta sun gudana a cikin wani yanayi mai kyau, in ji tawagar MANUL a cikin wata sanarwa.

Bangarori masu ruwa da tsaki sun jaddada tunaninsu cewa wannan wata dama ce domin amincewa da shirin sasantawa wanda zai kawo karshen rikicin kasar na yanzu, in ji mista Leon tare da bayyana cewa bangarorin na fatan ganin an kammala sasantawa nan da makwanni uku masu zuwa. Kammala shirin tattaunawa zai taimaka wajen cimma wata yarjejeniyar siyasa ta karshe a kasar Libiya da kuma aiwatar da ita a farkon watan Satumba, in ji MANUL.

Kasar Libiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan faduwar gwamnatin Mouammar Kadhafi a shekarar 2011, lamarin da ya kara tura kasar cikin rikicin kungiyoyin mayakan sai kai dauke da manyan makamai, haka kuma kasar ta rabu gida biyu a hukumance, kungiyar IS na kokarin neman gindin zaman a wannan kasa. A halin yanzu Libiya na da gwamnatoci biyu da majalisun dokoki masu gaba da juna. Daya a birnin Tripoli a karkashin kungiyar Fajr Libiya, kawancen mayakan sa kai da kungiyoyin kishin islama, kana kuma dayan a birnin Tobrouk dake gabashin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China