Kafin bude taron kusoshin kungiyar tarayyar kasashen Afirka karo na 25, Mark Suzman ya bayyana cewa, Sin ta taka muhimmiya rawa a wajen bunkasuwar duniya, musamman ma a fannonin aikin noma, kiwon lafiya, likitanci da sauransu. Fasahohin Sin sun zama abin koyi ga kasashen Afirka wajen samun ci gaba, ta yadda za su sami darussa daga cikinsu.
Ban da haka, Mark Suzman ya gano cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, Sin ta gudanar da ayyuka da dama domin taimakawa kasashen Afirka, kamar kafa cibiyar gwada fasahar aikin noma da sauransu. Ya nuna babban yabo kan wannan batu, tare da cewa, asusun Bill & Melinda Gates zai karfafa hadin gwiwa tsakaninsa da Sin a fannonin kiwon lafiya da raya aikin noma a kokarin taimakawa kasashe masu tasowa da wadanda ke fama da talauci, musamman ma kasashen Afirka baki daya.(Fatima)