in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin ya halarci bikin bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin shugabannin matasan Sin da Afirka karo na 3
2015-03-29 18:16:37 cri

Ranar Asabar 28 ga wata, Wang Jiarui, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya halarci bikin bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin shugabannin matasan kasashen Sin da Afirka karo na 3 a birnin Arusha na kasar Tanzaniya, inda kuma ya gana da shugaba Jakaya Kikwete, na Tanzaniya da shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, wanda ya halarci bikin a matsayin shugaban kungiyar tarayyar Afirka a wannan zagaye.

A yayin bikin, mista Wang ya yi jawabi mai lakabin "inganta dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka, a kokarin samar da kyakkyawar makoma ga bangarorin 2", inda ya bayyana cewa, Sin da Afirka suna kasancewa tamkar zarafi ne ga juna. Makomar huldar da ke tsakanin Sin da Afirka ta dogaro da matasa. Ana fatan matasan Sin da Afirka za su himmantu wajen raya kasashensu da kuma kyautata hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Shugaba Kikwete da shugaba Mugabe sun yaba da bude wannan taron dandalin, sun kuma yi fatan cewa, matasan Sin da Afirka za su gada da kuma inganta zumuncin gargajiya da ke tsakanin Sin da Afirka, a kokarin kara azama kan bunkasuwar huldar abokantaka irin ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China