Rundunar sojin Nigeriya a ranar Laraban ta ce, rahotanni daga kafofin watsa labarai na zargin hallaka wassu mutane har 150 da kungiyar Boko Haram ta yi tare da jefa su a cikin ruwa a garin Kukuwa-Gari a jihar Yobe ba gaskiya, ba za'a iya tabbatar da shi ba.
Rahotannin dai a wassu kafofin watsa labarai sun ce, fiye da mutane 150 ne kungiyar ta kashe tare da jefa su cikin kogi, abin da kakakin sojin wajen Kanar Sani Usman ya tabbatar wa al'umma cewar, rundunar tana yin iyakacin kokarinta na yaki da wannan kungiya, da kuma ganin an samar da zaman lafiya ga al'umman wannan yankin.
Ya kara da cewa, sojoji yanzu haka sun damke mutane 2 dake kokarin tserewa, wadanda kuma tabbas mambobin kungiyar ne a cikin motoci biyu a kori kura a garin Geidam na jihar ta Yobe.
A cewar kakakin sojin, wadanda aka kame yanzu haka ana masu tambayoyi. Haka kuma kanar Usman ya ce, yanzu haka akwai rahotanni da kiran neman dauki da suka samu game da 'yan kungiyar ta Boko Haram da kuma shirin kai hari da suke yi a wuraren Damasak. (Fatimah)