Wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram sun tuntubi gwamnatin Najeriya ta hannun wata kungiya mai zaman kanta domin bude wata hanyar tattaunawa da kawo karshen tashe-tashen hankali a wasu yankunan kasar, in ji wata majiya mai tushe a ranar Talata.
Komanda mai ritaya Yusuf Anas, babban sakataren cibiyar sasanta rikici (CCC), ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja cewa, tawagarsa da shi kansa suna nan suna tattaunawa kan shirya wani taro tare da hukumomin gwamnatin da abin ya shafa.
Mista Yusuf Anas, da ke magana gaban 'yan jarida kan batutuwan da suka shafi harkokin cikin gida, kamar matsalar ta'addanci, satar dabbobi, ricikin siyasa a majalisar dokoki, satar mai, sace-sacen mutane, fashi da makami da dai sauransu, ya bayyana cewa wannan sabon ra'ayi yana da muhimmancin gaske ganin cewa matakin amfani da karfin soja kadai bai warware matsalar ba.
Ya kawo goyon bayansa ga sanarwar shugaba Muhammadu Buhari da ya nuna cewa gwamnatinsa a shirye take ta tattauna tare da shugabannin kungiyar Boko Haram.
Cibiyar CCC ta bayyana cewa ana bukatar wannan tattaunawar ta gudana a tsanake ba tare da garaje ba, kuma kowa ya rike nauyin da bisa wuyansa, tare da la'akari da yunkurin tattaunawa na baya da aka kasa samun nasara, in ji mista Anas.
Da yake tabo tashe-tashen hankalin masu tsanani da rashin imani da kungiyar Boko Haram ta aikata a kan 'yan Najeriya da ma Najeriya, ya ce wannan abu ne mai wuya da amince da shi. Amma kuma sanarwar shugaba Buhari ta baya bayan na cewa gwamnatinsa na fatan bude shawarwari tare da mambobin Boko Haram, na kasancewa wani fatan alheri ga samun zaman lafiya, in ji shugaban CCC.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin dai mutuwar dubban mutane tun lokacin kafuwarta a shekarar 2009, haka kuma kungiyar ta ci gaba da zafafa hare-harenta tun bayan rantsuwar kama aikin shugaba Buhari a cikin watan Mayun da ya gabata, tare da janyo jerin hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 800 a cikin kusan watanni biyu kawai. (Maman Ada)