in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram 117
2015-07-31 09:27:42 cri

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram a kalla 117 a yankin tafkin Chadi.

Babban hafsan sojojin kasar ta Chadi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema. Ya kara da cewa, sojojin sun kuma yi nasarar lalata tare da gano wasu makamai da kwalale daga mayakan na Boko Haram.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, mayakan na Boko Haram sun kashe sojojin Chadin guda biyu, kana biyu kuma sun jikkata.

A makonni biyun da suka gabata ne dai sojojin na Chadi suka yi arangama da mayakan na Boko Haram bayan da suka kuste cikin yankin tafkin Chadi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China